Gommai sun mutu a hatsarin jirgi a Indiya
June 2, 2023Shaidun gani da ido da jami'ai sun shaidawa kafafen yada labarai na cikin gida cewa, jirgin fasinja na Coromandel Express da wani jirgin dakon kaya sun yi karo a kusa da Balasore mai tazarar kilomita 200 daga Bhubaneswar babban birnin jihar.
Kazalika hatsarin ya kuma ritsa da wani jirgin fasinja na biyu, a cewar babban sakataren Odisha Pradeep Jena, amma har yanzu ba a fayyace yadda lamarin ya kasance ba.
Sai dai wasu jami'ai da ba a bayyana sunayensu ba sun ce kimanin mutane 50 ne ake fargabar sun mutu, a yayin da wasu fasinjoji da yawa ke makale a karkashin jirgin dakon kayan.
Ofishin mataimakin sufeto janar na ‘yan sandan Balasore ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa akalla mutane 200 ne sun jikkata, kuma yawancinsu munanan raunuka.