1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hezbollah ta yi gargadi kan rikicin Siriya

May 1, 2013

Shugaban kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai gwagwarmaya da makamai, Sheik Hassan Nasrallah, ya ce 'yan tawayen kasar Siriya ba su da karfin kifar da gwamnati.

https://p.dw.com/p/18PzP
Hoto: Joseph Eid/AFP/Getty Images

Shugaban kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon mai gwagwarmaya da makamai, Sheik Hassan Nasrallah, ya ce 'yan tawayen kasar Siriya ba za su iya kifar da gwamnatin Shugaban Bashar al-Assad da karfi ba. Kana ya yi gargadin cewa kawayen kasar ta Siriya, a shirye su ke wajen tallafawa dakarun gwamnatin Assad.

Hassan Nasrallah ya kara da cewa ba za su zuba ido kasar ta Siriya ta fada hannun Amirka, Izira'ila da sauran masu zazzafan ra'ayi ba.

A wani labarin kuma, kimanin mutane 13 sun hallaka sakamakon hari da bam a Damascus babban birnin kasar ta Siriya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi