Neman shigowa Turai ko ta wacce hanya
April 29, 2015Bakin hauren da suka tsira da rayukansu sun dauki wannan matakin ne ta hanyar hada kai da hukumomin kasar a dai-dai lokacin da ake fama da badakalar mutuwar bakin haure da ke bi ta barauniyar hanya ta cikin sahara da teku domin shiga Turai. Daya daga cikin wadannan mutane mai suna Eric Opoku ya bayyana cewan ya dade da burin shigowa Turan inda ya ce....
"Na kasance da burin zuwa Turai tun daga makaranta, domin mahaifan abokaina da ke Turai da suke kawo musu kayan kyale-kyale da motoci da sauransu, dan haka ne na dage sai na shiga Turai duk da cewa bani da wanda zai gayyace ni ko kuwa ya tsaya mini."
Yanke shawarar bi ta teku bayan gaza samun Visa
Opoku da ke da shekrau 35 a duniya ya ce bayan duk yunkurinsa na samun visa ya ci tura, sai kawai ya dauki damarar biyowa ta tekun Bahar Rum, sai dai ya ce akwai hadarin gaske dangane da biyowa ta barauniyar hanyar yana mai cewa...
"A gaskiya akwai hadari kuma mun sha wuya sanda muka yanke shawarar dawowa, hasali ma fitsarinmu muka rinka sha don tsananin kishiruwa."
Shi kuwa Ernest Lawey daya daga cikin bakin hauren wadanda suka yi sa´ar komawa gida cewa ya yi...
"Mun tashi ne daga garin Bawku na arewacin Ghana zuwa kasar Gabon zaune a saman motar dakon kaya, daga nan ne muka karasa zuwa Libiya, kuma sai da muka biya kudi aka nuna mana hanya."
Hada karfi waje guda domin shawo kan matsalar
Duk da samun shiga kasar Libya lami lafiya, hukumomin kasar sun cafke su suka koma da su gida. Opoku Ware ya bayyana cewa a yanzu ma yawancinsu da suka koma gida sun fi samun rayuwa mai inganci a Ghana. Hukumar kula da matasa ta Ghana ta yi wani shirin hadin gwiwa da Eric Opoku Ware da Ernest Lawey domin wayar da kan matasa ko a samu karancin bakin haure da ke zuwa sun hallaka a Tekun Bahar Rum a kokarinsu na shigowa Turai da suke yiwa kallon "Tudun mun tsira" musammanma matasa.