Hillary Clinton ta baiyana buƙatar Amurika ta ƙarfafa ma'amala da Najeriya.
August 9, 2012A cigaba da rangadin aikin kwanaki 11 dfa ta kai a Afirka, Sakatariyar harkokin wajen Amurika Hillary Clinton ta gana a wannan Alhamis da hukumomin Naeriya.
Masu sharhi game da Afrika, na fasara rangadin na Clinton a Afirka a wani yunƙurin Amurika na ƙara samun angizo a nahiyar, a daidai lokacin da ƙasar China ke ƙara samu gindin zama.
A duk ƙasashen Afrika da Hillary Clinton ta ziyarta ta tattana da magabatan game da batutuwa masu mahimmanci, wanda suka jiɓanci kare 'yancin bani Adama, demokraɗiyya da kuma ma'amala tsakanin Amurika da wannan ƙasashe, tare da yin hannunka mai sanda ga shugabanin ƙasashen dangane da ma'amalarsu da China.
Ita dai ƙasar ta China saɓanin Amurika,ta na bada tallafi da ƙasashen Afrika ba tare da yin la'akari ba da batutuwan da suka shafi demokraɗiya ko kuma kare 'yancin bil Adama.
A tsukin shekaru goma da suka gabata, ƙasar China ta samu karɓuwa matuƙa a Afrika, al'amarin da ya fara dusashe angizon ƙasashen Turai da Amurika.
Jakkie Cilliers manazarci ne a cibiyar tsaro dake birnin Pretoriya na Afrika ta Kudu, ya bada dalilan hammayar mai tsanani tsakanin China da Amurika a nahiyar Afrika:
" Hammaya tsakanin Amurika da China a nahiyar Afrika ta ƙarfafa domin ko wace ƙasa daga cikinsu na buƙatar ƙulla dangatakar kasuwanci.Yanzu Afrika ta daina zama 'yar amshin shata a fagen siyasa da kasuwanci na duniya , ta rikiɗa zuwa wata babbar kasuwar duniya, wadda kowa ke buƙatar samun abokan hulɗa."
China tare da haɗin gwiwa da ƙasashen Brazil, Rasha, Indiya da Afrika ta Kudu sun kafa wata ƙungiyar ƙasashe masu tashe ta fannin bunƙasar tattalin arziki da suka raɗawa suna BRICS.
Manahajojin wannan ƙungiya sun sha bambam da tsarin da aka sani irin na turawan mulkin mallaka da Amurika game da ma'amala tsakanin su da Afrika.Tallafin da suke baiwa ƙasashen Afrika irin na sha yanzu biya yanzu, saɓanin Amurika da Turai, inda sai an jima ana tafka dogon turanci, tare da gitta sharuɗan da sai ƙasa ta cika su.
Hatta cikin 'yan kwanakin nan ,Amurika ta yanke shawara dakatar da taimakawa Ruwanda dalili da zargin da ta ke wa gwamnatin Kigali na haɗa kai ada 'yan tawaye domin tada fitina a Jamhuriya Demokraɗiyar Kongo.
Philipp Gieg manazarcin al'amuran siyasar ƙasa da ƙasa ne a jami'ar Würzburg dake nan Jamus wanda a tunaninsa akwai kura-kurai da muna-muna a cikin ma'amala tsakanin Amurika da Afrika kuma ya bada hujjoji:
"Amurika na matsa ƙaimi ga ƙasashen Afrika, game da wajibcin tabbatar da demokraɗiyya da kare 'yancin bani Adama, to amma ta nuna bambanci a cikin al'amarin,ɗauki misali da ƙasar Ethiopiya wadda ta yi ƙaurin suna ta fannin take haƙƙoƙin jama'a da kuma tauye demokraɗiyya, amma Amurika ba ta taba daga yatsa ba domin tsawatama hukumomin ƙasar."
Bincike da wata cibiyar nazari ƙungiyar tarayya Turai ta gudanar ya gano cewar Afrika na cin moriyar kashi 46 cikin ɗari na kuɗaɗen taimakon raya ƙasa da China ke kashewa ko wace shekara, ta fannin gine-ginen hanyoyi asibitoci makarantu da dai sauran aiyukan cigaban ƙasa.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu