Hillary Clinton ta gana da Hussain Tantawi
July 15, 2012A ci gaba da ziyarar da take yi a kasar Masar sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta gana da shugaban rundunar sojin kasar, Field Marshal Hussain Tantawi inda ta yi kira gareshi da mukarrabansa da su dafa wajen ganin tsarin demokradiyyar kasar ya samu gindin zama. Uwargida Hillary ta ce hakan zai taimaka wajen ciyar ta kasar gaba musamman ma dai ta bangaren tattalin arziki. Baya ga haka ta kuma gana da wakilan Kiristoci Kibdawa na kasar ta Masar inda ta jaddada kudurin Amirka na kare hakkin dukannin al'ummar kasar: Maza da Mata, Musulmi da Kiristoci baki daya.
Ziyarar ta Uwargida Hillary wadda ke karewa a yau na zuwa ne daidai lokacin da ake sa in sa tsakanin sabon shugaban kasar Muhammad Mursi na jam'iyyar 'Yanuwa Musulmi da kuma jagoran majalisar kolin sojin kasar Field Marshal Hussain Tantawi musamman ma dai batun jan ragamar madafun ikon kasar.
Mawallafi. Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas