1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hillary Clinton ta ziyarci Sudan ta Kudu

August 3, 2012

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun gaza cimma matsaya a rikicin da suke yi a kan iyaka.

https://p.dw.com/p/15jVy
epa03337058 South Sudanese President Salva Kiir (R) greets US Secretary of State Hillary Clinton (L) in Juba, South Sudan, 03 August 2012. Secretary Clinton arrived in Juba early 03 August as part of her African tour, during which she is visiting Uganda, Kenya, South Sudan, Malawi, Nigeria, Benin and South Africa to promote the United States strategy in regards to Sub-Saharan Africa. EPA/PHILIP DHIL
Hoto: picture-alliance/dpa

A yau Juma'a ne sakatariyar harakokin wajen Amirka Hillary Clinton, ta kai wata ziyara a sabuwar kasar Sudan ta Kudu a rangadin da ta fara a Afrika, inda za ta gana da shugaba Salva Kiir a kan wasu muhimman batutuwa ciki har da batun gaugauta samun daidaito da makwabciyar kasar Sudan ta shugaba Albashir a kan rikicin kan iyaka da na ma'adanun man fetur.

A jiya ne a ka kai karshen wa'adin biyu ga watan Augusta da Majalissar Dinkin Duniya ta baiwa kasasahen biyu na su cimma yarjejeniya a kan batutuwan da suka haddasa rikicin.

To saidai kawo yanzu kasashen guda biyu sun kasa samun daidaito a tautaunawar da suke yi a karkashin jagorancin kungiyar gamayar Afrika ta AU.

A shekarar bara ne dai kasar ta Sudan ta Kudu ta samun 'yancin gashin kanta daga Sudan bayan kazamin yakin da a ka share shekaru sama da 25 suna gobzawa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Abdullahi Tanko Bala