Tattalin arziki
Matashi mai sana'ar sayar da burodi
August 25, 2021Talla
Matashin mai suna Ali Dahiru Garga dai, na shiga lungu da sako domin sayar da burodin nasa. Ya ce ya dade yana neman aiki amma a karshe sai yaga yana batawa kansaa lokaci ne, hakan ya sanya ya fara wannan sana'ar. Ali ya ce ya fara sana'ar sayar da burodi a kan babur da burodi 50, to amma yanzu a kowace rana yana yin safarar guda 400. Ya ce ya samu nasarori masu tarin yawa, koda yake akwai kalubalen da ba za a rasa ba. Matashin ya kuma shawarci 'yan uwansa matasa, a kan su tashi tsaye domin neman na kansu.