Hukumar EFCC ta cafke wasu tsoffin gwamnoni 2 a Najeriya
July 12, 2007Talla
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta taraiyar najeriya ta cafke wasu tsoffin gwamnoni guda biyu.
Kakakin hukumar Osita Nwajah yace hukumar ta tsare tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu da Saminu Turaki na jihar jigawa.
Yace yanzu haka ana tuhumar tsoffin gwamnonin biyu game da zargin rubda ciki da kudin alumma da karkata akalar dukiyoyin jamaa da halalta kudin haram.