Hukumar samarda abinci tace miliyoyin yan Koriya ta arewa ke fuskantar yunwa
October 16, 2006Talla
Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta sanarda cewa miliyoyin yan kasar Koriya ta arewa suke fuskantar matsananciyar yunwa a lokacin hunturu na bana saboda raguwar taimakon abinci zuwa kasar.
Kodayake takunkumi da komitin sulhu ya lakabawa Koriyan bai shafi kayan abinci ba,amma hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya tace Amurka ta sanarda janye taimakon abinci da take baiwa Koriyan ta hannun majalisar hakazalika Koriya ta kudu ta dakatar da bada nata taimako haka kuma kasar Sin ta rage nata taimakon zuwa kashi daya bisa uku.