Hukumar zabe a Kenya ta bayyana sakamakon zaben raba gardama
November 22, 2005Hukumar zabe mai zaman kanta a kasar Kenya ta bayyana sakamakon zaben jin ra´ayin jama´a da a ka gudanar jiya, a game da kundin tsarin mulki na kasa.
Sakamakon wannan zabe ya nuna cewa masu adawa da wannan kundi, sun samu gagaramar nasara ,tare da kuri´u kimanin million 3 da rabi, a yayin da masu shelar amincewa da shi, su ka tattara kuri´ u kussan million 2 da rabi.
Baki mutane million 11 ne dubu dari shidda, ya cecenta su kada kuiri´un raba gardama a game kudin.
Duk da cewa ya zuwa yanzu, ya rage sauran mazabu 10, da ba a bayyana sakamakon su ba, babu tababa ,yan bangaren watsi da kundin sun samu nasara.
Saidai ko jama´a ta amince, ko kar ta amince da wannan kwaskwarima, shugaban kasa Mwai Kibaki, ya ce ba zi shi murabus ba, daga mukamin sa.
A lokacin yakin neman zabe ya dage ,a kan kiran jama´a da ta bada goyan baya ga saban kudin, domin cenza tsarin mulkin da kasar ta gada tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Shugaban ya bayyana wannan daftari a matsayin ginshinkin Demokradiya da kare hakokin jama´a, da kuma habaka tattalin arzikin kasa.
Saidai masu adawa da shi, na zargin saban daftarin da tattara mulki a cikin hannun shugaban kasa, ta hanyar ba shi wuka da nama a game da dukan al´ammurra.
Rahotani daga Kenya, sun tabbatar cewa mutane da dama sun hallarci runfunan zabe, kuma komi ya gudana salin alin, illa kawai, yan rigingimmu da ba za a rasa ba, nan da cen, wanda ba su kawo cikas ba, ko mici kala zaratin.
An jibge jami´an tsaro kimanin dubu 50 a fadin kasar baki daya cikin shirin ko ta kwan, don riga kafi ga tashen tashen hankullan da su ka wakana a lokacin yakin neman zabe, inda a kalla mutane 8, su ka rasa rayuka tare da jimuwar wasu da dama.
Kakakin hukumar zabe mai zaman kanta ya tabatar da, a jimilce za a iya cewa, an gudanar da zaben cikin adalci, da kwanciyar hankali, sabanin yadda mutane da dama su ka zata da farko.
Ta fannin siyasa, saban kundin tsarin mulkin ,ya haddasa rarabuwar kanu, hatta a cikin gwamnati, inda wasu daga ministoci su ka yake shi, sabanin shugaban kasa da mafi yawan ministoci.
Jam´iyun adawa, da kungiyoyin addinai, bisa dogaro da hujjoji da su ka sabawa juna, sun nuna kyamar kundin.
Masu kulla da harakokin siyasa a kasar Kenya sun nunar da cewa, sakamakon zaben, zai cilastawa shugaban kasa yin garambawul ga gwamnati.
Wasu manazartan ma, na tunanin cewa, kamata ta yi Mwai Kibaki ya yi murabus daga mukamin sa, domin watsi da saban kundin tsarin mulkin tamkar janye masa amanar jan ragamar kasa ne, jama´a ta yi.