1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi da hukumar zaben Najeriya sun gana

Uwais Abubakar Idris SB/AH/LMJ
February 21, 2023

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya da kungiyoyin saka ido kan zabe sun gana game da zaben da za a yi a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4NmyF
Najeriya I Lagos gabanin zaben shugaban kasa
Shirye-shiryen zaben NajeriyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ya gana da kungiyoyin da za su saka ido a zaben Najeriyar da za a yi a karshen mako, inda ya gargade su da su guji katsalandan a kan harakar zaben Najeriya su tsaya a kan aikinsu na saka ido tare da kare mutuncin Najeriya a matsayinta na  kasa mai ‘yanci.

Karin Bayani:Shirin gudanar da babban zaben Najeriya na 2023 ya kankama

Ganawa ce dai keke da keke a tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya da wakilan kungiyoyin na cikin Najeriya da na kasashen waje da ke sa ido a kan zaben da za a fara a karshen mako. An karanto masu jerin kaidoji na aikin da suke yi bisa radin kansu amma da amincewar gwamnati abinda ya sanya aka yi masu rijista don amincewa da su.

Najeriya Zabe
Shirye-shiryen zaben NajeriyaHoto: DW/Gänsler

Hukumar zaben Najeriyar xce dai ta gayyaci masu sa ido a kan zaben a matsayin hanyar da zai taimaka tabbatar da sahihancinsa daga aikin da zasu yi bayan sun sanya ido a kan zabe. A zaben na wannan shekara a Najeriyar hukumar zaben ta yiwa masu sa ido a zaben rijista na cikin gida 146, 913 wadanda suka baza jamiansu 144,800 baya ga kungiyoyin kasa da kasa 33 da aka yi wa rijista wadanda suka turo masu sa ido 2,113. Wannan ce tawaga mafi girma a tarihin zabe a Najeriyar.

Mafi yawan masu sa ido a kan zaben na Najeriya sun jadada bukatara gudanar da shi cikin zaman lafiya da kwanciyara gankali da kaucewa batu na rufa-rufa da ma sayen kuru'u da zasu iya shafar zaben na Najeriya. Duk da kalubalen da ake fusknata hukumar zaben da shugabanin hukumomi tsaro sun bayyana tabbacin cewa za'a  sun kyautata yanayin tsaro don tabbatara da an gudamar da zaben da duniya ta sanya Najeriyar idanu don tabbatara da kyautata tsarin da kasar ta dade tana tinkahon ta samu.