Hukumcin kisa a kan wasu baƙi a Gambiya
August 28, 2012Talla
Matamaikin diraktan ƙungiyar reshen Afirka Paule Rigaud a cikin wata sanarwa da ya baiyana,ya ce sun yi mammakin yadda gwamnatin Gambiya ta aiwatar da hukumcin na kisa wanda ya ce yin hakan ya saɓama dokokin kare haki bil addama.
A ranar lahadin da ta gabata ne ofishin minista cikkin gida na Gambiya ya ba da sanarwa cewa an kashe mutane guda tara a ciki hada macce ɗaya ta hanyar bindige wa. Tun farko shugaban ƙasar Yahya jammeh ya sanar da cewar zuwa tsakiyar watan Satumba;za su kashe dukanin mutane da ake tuhuma guda 47 galibi yan ƙasahen waje.Duk kuwa da kiraye kirayen da ƙungiyar Tarrayar Afirka da Tarrayar Turai suka yi na a dakatar da kisan.
Mawallafin: Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi