1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomi a Saudiyya sun kame masu kishin Islama sama da 130

December 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuZJ
Ma´aikatar harkokin cikin Saudiyya ta ce a cikin watani 3 da suka gabata jami´an tsaron kasar sun kame mutane 136 wadanda ake zargin cewa musulmi ne ´yan ta´adda. Kamfanin dillancin labarun kasar ta Saudiyya SPA ta rawaito ma´aikatar cikin gidan na cewa an kame mutanen ne a jerin samame da aka kai a duk fadin kasar. Daukacin wadanda aka kamen dai ´yan kasar ta Saudiyya ne wadanda ke cikin wasu kungiyoyi masu alaka da kungiyar ´yan ta´adda ta al-Qaida. Daya daga cikin kungiyoyin kuwa na shirin kaiwa wani hari ne, inji ma´aikatar.