Hukumomin Nijar sun karfafa matakan tsaro tun bayan harin Agadez
May 31, 2013
A game da koken-koken kungiyoyin fararen hula kan karfafamatakan tsaro,ministan cikin gida na Nijar ya shirya wani babban taron gangami a birnin Yamai tare
da hadin gwiwar shugabannin hukumomin tsaro da wakillan al'umma domin yin baiyani game da dalillansu na daukar matakan da ma kuma neman goyan bayan al'umma a cikin aiwatar da wanann mataki.
Tun dai bayan abkuwar hare-haren ta'adancin da aka kai a jihar Agadez a makon da ya gabata, hukumomin tsaro su ka kara kaimi ga matakan tsaron da su ka dauka a baya, a kusan duk fadin
kasar a lokacin rikicin kasar Libiya da na Mali da ma na Boko-Haram Najeriya.Yanzu haka dai hukumomin tsaron sun kara baza
jami'an tsaro a cikin manyan biranan kasar, inda a gurare da dama su ka datse hanyoyi da binciken ababan hawa a bakin wasu ofisoshin dama a duk a wasu guraran da su ke da shakku akansu a cikin gari.To sai dai tuni wasu kungiyoyi su ka soma nuna damuwarsu da matakin da su ka ce jami'an tsaron na wuce gona da iri wajen aiwatar da matakan tsaro.A cikin wata sanarwa da ta fitar kawancen kungiyoyin fararan hula na "CADRE" ta bakin shugabansa Abdulmumuni Usmane, ya nuna damuwarsa dangane da
yanda lamarin binciken ke wakana a cikin jahar Agadez.
Ko a birnin Yamai ma dai duk kanwar ja ce, gwamnatin ta karfafa
matakan tsaro a bakin wasu manyan ofisoshinta da na jakadancin
kasashen waje.Majalissar dokokin kasar Nijar na daga cikin
irin wadannan gurare, inda yanzu haka aka haramta shigar duk wani abun hawa na duk wasu mutanan da ba ma'aikatan gurin ba ne ko ma kuma 'yan Majalisa.
Ganin irin yanda wadannan korafe-korafe ne ma su ka soma yin yawa ya sanya Ministan cikin gida Malam Abdu Labo ya kira wani babban taron gangami a birnin Yamai, inda ya bayyanawa al'umma dalilansu na daukar wadannan matakai, da kuma neman goyan bayan al'ummar ga wanann shiri.
Yanzu haka dai gwamnatin ta bada sanarwar gudanar da irin wadannan taruruka na fadakarwa a duk jahahohin kasar da zummar samun goyan bayan al'umma ga wadannan matakai da yace na sabke gyran kayanka ne da ba zai taba zama aje mu raba ba.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi