1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama wasu 'yan Najeriya da laifin tallafawa Boko Haram

Mahmud Yaya Azare RGB
November 12, 2020

Wata kotun daukaka kara a Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu 'yan Najeriya da aka samu da laifin tallafawa Kungiyar Boko Haram da kudadden gudanar da aiyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/3l77q
Vereinigte Emirate Abu Dhabi | Besuch Putin | Mohammed bin Zayed Al Nahyan
Hoto: Alexei Nikolsky/picture-alliance/dpa

Kotun daukaka kara a Hadaddiyar Daular Larabawa ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga 'yan Najeriya guda shida ne bayan samunsu da laifin bai wa Kungiyar Boko Haram kudade don su gudanar da harkokin ta'addaci a yayin da dangin wadanda abun ya shafa suka ce bita da kulli ne. Mutanen goma dai 'yan Najeriya kotun ta yankewa hukunci, shida daga cikinsu wadanda aka tabbatar da cewa, 'yan gani kashenin Kungiyar ta Boko Haram ne, an yanke musu hukuncin daurin rai da rai, a yayin da sauran hudun da ba 'yan kungiyar bane aka daure musu hukuncin daurin shekaru goma goma.      Karin bayani: Hukuncin rai da rai a Najeriya

Sama da miliyan daya sun rasa muhallinsu a sakamakon rikicin Boko Haram

Symbolbild I Nigeria I Islamisten nehmen Geiseln
Boko Haram ta raba mutum sama da miliyan daya da gidajensu a NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Sunayen biyu daga cikin wadanda aka yanke ma hukuncin daurin rai da rai, sun hada da Surajo Abubakar Mahmud da Saleh Yusuf Adamu, yayin da sauran 4 kuma da aka daure shekaru goma a gidan yari suka hada da Ibrahim Ali Alhassan da Abdurrahman Ado Musa da Bashir Ali Yusuf da kuma Muhammad Ibrahim Isa.Tun a bara ne aka kame wadannan mutanan aka kuma fara shari'arsu, yadda bayan daukaka kara, kotun daukaka karar ta yanke wannan hukuncin. Kotun dai ta ce, Waɗanda aka ɗaure ɗin na da hannu wurin tura wa Boko Haram kuɗi kusan dala 782,000 a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016. 

Yan'uwan wadanda aka daure sun ce kagen abokan hamayyar kasuwanci ne

Nigerien Boko Harams Führer Abubakar Shekau
Mayakan Boko Haram karkashin Abubakar Shekau sun hallaka dubbai a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo

 Sai dai iyalai da kuma abokan mutanen da aka yankewa wannan hukuncin, sun ce hukunci bai rasa nasaba da shune irin na mahassada da abokan hamayyar kasuwanci da suka ga wadannan mutanan da ke harkar chanji liyafarsu tayi gaba. A shekarar 2017 ne dai Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya cimma yarjejeniyar musayan fursunoni da Daular Larabawa. A bara ma dai an yankewa wasu 'yan Najeriya hukuncin kisa kan laifukan fashi da makamai da fataucin hodar iblis. Hadaddiyar Daular Larabawa wacce a 'yan shekarun bayan nan ake zarginta da zama tungar masu hallata kudin haram, ta tashi haikan wajen nesan ta kan ta da wannan zargin, inda take kuma daukar matakan ba sani ba sabo kan miyagu da masu hallata kudin haram a kasarta.