Hukuncin kotu kan rikicin jam'iyyar MNSD
July 23, 2015A jamhuriyar Nijar kotun daukaka kara wato Cour d'Appel ta birnin Yamai ta karya matakin da ya haramtawa bangaran Albade Abuba tsohon magatakardan jam'iyyar MNSD Nasara yin magana da sunan jam'iyyar. Kotun ta bayyana haka ne lokacin wani zama da ta gudanar a wannan Laraba.Tuni dai Bangaran Albade Abuban ya bayyana gamsuwarsa da wannan hukunci .
Sai dai rikicin shari'ar jam'iyar MNSD Nasara dake adawa,tsakanin shugaban jam'iyar na kasa Alhaji Seini Umaru,da bangaren Albade Abuba bai kare ba,inda yanzu haka suke jiran sakamakon wata shari'ar a kan wani karan da bangaren Alhaji Seini Umaru din ya shigar a gaban kotun koli mai hurumin karya shari'a wato Cour de Cassation.
Rikicin Jam'iyyar ta MNSD Nasara madugar jam'iyyun adawar kasar ya samo tushe ne tun a lokacin kafa gwamnatin hadin kan kasa inda bangaren Albade Abuba ya karbi tayin shiga gwmnati a yayinda bangaren Seini Umaru ya kauracewa tayin a bisa hujjar cewa ya sabawa doka.