Hungary: Matsaya kan shigar Sweden kungiyar NATO
February 26, 2024Talla
Ana sa ran 'yan majalisar za su kada zaben amincewa da bukatar Sweden din na zama mamba a kungiyar a NATO, ko da yake tuni kwamittocin majalisar suka amincewa da hakan.
Dama dai Hungary ce kasa ta karshe cikin kasashen mambobin kungiyar 31 a kungiyar ba ta amincewa Sweden din ba. Tun dai a watan Mayun shekarar 2022 ne dai kasar Sweden ta nemi shiga kungiyar ta NATO, sai dai ta fuskanci jinkirin amincewar kasashen Turkiyya da Hungary. A farkon watan Afrilun bara ce, aka amince da kasar Finland a matsayin mamba ta 31 a kungiyar.