1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illolin yakin duniya na farko a Afirka

Abdullahi Tanko Bala MAB
November 15, 2018

Shekaru 100 da suka gabata ne aka kawo karshen yakin duniya na farko bisa taimakon sojojin Afirka. Sai dai yakin ya bar baya da kura a kasashen da Jamus ta yi wa mulkin mallaka ciki har da Kamaru da Togo da Namibiya.

https://p.dw.com/p/38LTN
Die "Schwarze Armee" - Afrikaner im 1. Weltkrieg
Hoto: picture-alliance/Mary Evans Picture Library

A ranar Lahadi 11 ga watan Nuwamba ne aka cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na farko bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin dakarun Jamus da kuma dakarun kawance na sauran kasashen duniya. birnin Ypres da ke a yammacin Beljiyam na daya daga cikin wuraren da aka yi babban ta'adi a lokacin yakin duniya na farko, Yayin da a Afirka kasashen Birtaniya da Faransa suka raba Jamus da Togo da Kamaru. Hasali ma rabewar Kamaru ya sa ana fuskantar rikicin aware a halin yanzu.