Jamus: Makomar dangantaka da Afirka
January 16, 2025Hasali ma, fadar mulki ta Berlin na neman hadin kan wadanda za su gaji kujarar mulki da su aiwatar da sababbin manufofin da ta dauka din sau da kafa. Saboda matakin girmama junan da ya zamo jigo a huldar Jamus da Afirkan, Berlin din na bayar da fifiko ga laifuffukan da ta aikata a zamanin da ta yi wa wasu kasashen nahiyar mulkin mallaka. Shugabannin na Jamus sun yi alkawrin amince wa da aikata rashin adalci da biyan diya ga kasashen, tare da mayar da muhimman kayayakin tarihi da Turawan mulkin mallaka suka wawashe a yayin da suke kan ganiyarsu.
Karin Bayani: Jamus: Mayar da masu neman mafaka Senegal
Kuma a cewar kakakin jam'iyyar SPD mai mulki, ba zai yi wu a samar da wasu muhimman batutuwan kyautata alkiblar siyasar ketare a cikin wata sabuwar siga da nahiyar Afirka ba tare da yin waiwayen abubuwan da suka wuce na mulkin mallakar ba. Ita dai gwamnatin Jamus da ta wargaje ta dukufa tukuru wajen yekuwar kara wa nahiyar Afirka karfi da samar da daidaito a tsakaninta da kasashen duniya, ta dalilin haka ne ma dai ta kara matsa kaimi na ganin nahiyar ta kai ga samun wakilcin kujeru biyu na din-din-din a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
A yanzu dai kujeru uku ne kawai wadanda ba na din-din-din ba nahiyar Afirkan ke da su, kuma ake jujjuyawa daga wata kasar zuwa bayan shekaru biyu. A shekara ta 2019 ma dai, batun tsaro da samar da daidaito ya kasance babban jigo na gaba-gaba a manufofin sabuwar gwamnatin Olaf Scholz. Sai dai an juya musu baya, lokacin da Rasha ta soma mamayar da take yi wa makwabciyarta Ukraine. An maye gurbin wadannan manufofin zuwa ga batun alkinta muhalli, lamarin da ya sha suka daga wasu bangarorin jam'iyyun adawar Jamus kamar CUS da ke ganin an gaza in ji Wolfang Stefinger da ke zaman shugaban kwamitin huldar kasa da kasa da ci-gaban tattalin arziki na majalisar dokokin Jamus.
Karin Bayani: Namibiya: Diyya muke bukata ba tallafi ba
Barin wannan sarari ya kara habaka wagegen gibi a tsakanin nahiyar Afirka da Jamus, musamman a yankuna da dama a cewar masu adawa da gwamnatin Scholz. Daraktan kungiyar Jamusawa masu Kamfanoni da ke da Tsatso da Afirka Christoph Kannengiesser ya yi na'am da wannan batu, inda yake cewa a cikin yanayi na kyakkyawan fata da tasirin siyasar duniya da habakar tattalin arziki da Afirka ke da buri akai, gwamnatin Jamus na yin taka tsantsan. Batun zaben gabanin wa'adin da za a yi dai, haifar da ayoyoyin tambaya kan makomar alkiblar siyasar Jamus a nahiyar Afirka.