1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar bude kan iyakokinsu a Kashmir

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNM

Wadannan hare-haren dai sun zo ne a daidai lokacin da Indiya da Pakistan suka amince su bude kan iyakokinsu na Kashmir. Bayan shawarwarin da suka yi a birnin Islamabad, kasashen biyu sun sanar da bude wasu hanyoyi 5 akan layin da ya raba iyakokin su daga ranar 7 ga watan nuwamba. Ta haka za´a samu sukunin taimakawa dubban mutanen da girgizar kasar nan ta ranar 8 ga watannan na oktoba ta rutsa da su. A halin da ake ciki MDD ta yi lale maraba da wannan yarjejeniya da Indiya da Pakistan suka cimma ta bude kan iyakokin na Kashmir don taimakawa dubban mutane tare da kai kayan agaji. To amma MDD ta ce har yanzu ana fama da matsaloli wajen kai dauki ga miliyoyin mutane.