1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya na fafutukar yaki da 'yan ta'adda

Zulaiha Abubakar
February 12, 2018

Ministan tsaron kasar Indiya ta shaida wa manema labarai cewar 'yan kungiyar ta'adda ta Jaish-e-Mohammed da ke  kasar Pakistan ne suka kai mummunan hari a sansanin sojojin Indiya da ke yankin Kashmir

https://p.dw.com/p/2sYe6
Indien Ministerin Nirmala Sitaraman
Nirmala Sitaraman minista harkokin tsaro ta IndiyaHoto: Getty Images/AFP/M. Sharma

Ministan tsaron Nirmala Sitharaman ta kara da cewar New Delhi za ta gabatar wa da Pakistan shaidar da ta tabbatar da cewar Masood Azhar shugaban kungiyar 'yan ta'adda ne ya jagoranci  wannan mummunan hari daga nan sai ya kara da gargadi ga Pakistan cewar ta saurari abin da zai biyo baya.

A na ta bangaren hukumar tsaron Pakistan ta ce ba za ta ci gaba da amicewa da irin wanan zargi mara tushe da Indiya ta ke yi ma ta ba,shi dai yankin na Kashmir na rabe ne a tsakanin kasashen biyu yayin da kowacce kasa ta ke kurarin ita tafi cancanta ta mallaki yankin gabadaya.