1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jimamin mutuwar Dilip Kumar

Ramatu Garba Baba
July 7, 2021

Al'ummar kasar Indiya sun fada cikin jimamin rashin shahararren jarumin fina-finan Bollywood Dilip Kumar da ya mutu a wannan Laraba yana da shekaru 98 a duniya.

https://p.dw.com/p/3w8Kt
Indischer Schauspieler Dilip Kumar
Hoto: Rosland Rahman/AFP/Getty Images

Firaiminista Narendra Modi ya mika sakon ta'azziyarsa ga al'ummar kasar Indiya bisa rashin shahararren jarumin fina-finan kasar Dilip Kumar, da ya mutu yana da shekaru casa'in da takwas a duniya a wannan Laraba. Jarumin ya mutu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya a wani asibiti da ke birnin Mumbai.

Za dai a ci gaba da tunawa da jarumin da ya kwashi fiye da shekaru sittin yana fitowa a fina-finan Indiya daban-daban, da muhinmiyar rawar da ya taka a ci gaban masana'antar Bollywood. Fim din Dilip Kumar na farko shi ne Jugnu kuma na karshen shi ne Qila da yayi a shekarar alif da dari tara da casain da takwas.