Indiya ta hallaka 'yan bindiga da suka kai hari
January 3, 2016Wata majiyar 'yan sanda ta kasar Indiya ta ce a wannan Lahadi jami'an tsaron kasar sun yi nasarar hallaka mutane biyu na sauran mambobin rukunin 'yan bindigar da suka kaddamar da hari a sansanin sojojin kasar na Pathankot na cikin jihar Pendjab da ke a nisan kilomita 50 da kan iyakar kasar ta Indiya da makobciyarta ta Pakistan.
An kashe 'yan bindigar biyu ne a lokacin wata fafatawa da aka yi da su a wani filin jirgin sama na arewacin kasar.
A jimilce sojojin gwamnati bakwai da kuma 'yan bindiga shida suka rasu a cikin wannan harin da wasu 'yan bindiga da ake zaton mambobin wata kungiyar masu tsananin kishin addini ta kasar Pakistan ce mai suna Jaish-e-Mohammed suka kawo shi a cikin daren Jumma'a washe garin Asabar.
Yanzu haka dai jami'an tsaro na ci gaba da yin binciken kokop a sansanin sojin na Pathankot domin tabbatar da cewa babu sauran 'yan bindigar da suka boye a cikinsa.