Indiya ta kori jami'in jakadancin Pakistan
October 27, 2016A wani sanarwa da ministan harkokinn wajen Indiya Vikas Swarup ya aikewa hukumomin kasar ta Pakistan na cewar suna zargin jami'in Mahmood Akhtar da laifukan leken asiri da satar bayanan sojojin Indiya hada da mallakar takardun da ya shafi diplomaciyar kasar da ake takaddama a kan yankin Kishmir da kasashen biyu ke takaddama a kai.
To sai dai mahukuntar kasar Pakistan sun yi watsi da zargin, kuma sun dauki matakan korar jakadan Indiya da ke Pakistan. A yanzu dai Indiya ta baiwa Pakistan wa'adin sao'i 48 da su janye jami'in nasu daga kasar kana za su kwace takardan izinin zamansa a Indiya. A tun watan Satumban da ya gabata ne dai aka shiga tsamin dangantaka tsakanin kasashen Indiya da Pakistan bayan fada da ya barke tsakanin dakarun su a kan iyakar Kishmir yankin da dukkanin kasashen biyu ke ikirarin mallakarsa.