1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta samu sabon shugaba ƙasa

Usman ShehuJuly 22, 2012

A ƙasar Indiya Pranab Mukherjee ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, ya dai samu rinjaye daga zaɓen da majalisun jihohi da na ƙasa suka yi

https://p.dw.com/p/15d2t
Pranab Mukherjee in Kolkata, Pranab Mukherjee arrives at West Bengal Assembly on monday in kolkata to meet the left and congress leaders. Copyright: DW/Prabhakar Mani Kolkata, 9.7.2012
Pranab Mukherjee, Sabon shugaban ƙasar IndiyaHoto: DW

A Ƙasar Indiya an zaɓi Pranab Mukherjee a matsayin sabon shugaban ƙasa. Bayan kammala girga ƙuri'u da aka kaɗa a majalisun dokokin johohi dana ƙasa, an tabbatar da Mukherjee a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Mukherjee dai gogaggen ɗan siyasane, kuma daga cikin muƙamen da ya taba riƙewa harda na ministan kuɗi. Masu lura da siyasar ƙasar ta Indiya, suka sabon shugaban sai fi wanda ya gabaceshi yin hobbasa don warware rikicn da majalisar dokokin ƙasar ke fiskanta da kuma tabbatar da Indiya ta samu zaburar tattalin arziki, wanda kawo yanzu ke tafiyar hawainiya. Mukherjee ɗan shekaru 76 a duniya kuma wanda ke cikin jam'iya mai mulki ta Congress Party, ya kada abokin takaransa kana kakakin majalisar dokokin Indiya, P.A. Sangma, wanda babbar jam'iyar adawan ƙasar BJP ta marawa baya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh