Indiya ta tsaida kasuwanci da Pakistan
April 19, 2019Gwamnatin kasar Indiya dai na zargin hukumomin sojin kasar Pakistan da yin amfani da yankin Kashmir wajen safarar makamai da hodar ibilis da kuma kudin jabu.
Ministan cikin gida na kasar ta Indiya wanda ya sanar da daukar matakin ya ce za su ba da izinin komawa huldar kasuwancin kasashen biyu a wannan yanki a nan gaba bayan gwamnati ta kafa wani tsarin bincike mafi inganci.
A shekara ta 2008 ne a wani yinkuri na kyautata huldarsu kasashen biyu wadanda sau uku suna gwabza yaki, biyu kan batun yankin na Kashmir tun bayan samun 'yancin kansu suka cimma yarjejeniyar yin amfani da wannan yanki wajen safarar kayan abinci da na marmari zuwa kasashen juna.
A watan Fabrerun da ya gabata ma dai sun kai wa juna hari ta sama biyo bayan wani harin kunar bakin wake da ya halaka jami'an tsaron kasar ta Indiya guda 40.