Indiya tayi gwajin makami mai linzami
October 5, 2007Talla
Kasar Indiya tayi gwajin wani makami mai linzami na nukiliya mai gajeren zango a jihar Orissa dake gabacin kasar.Wannan shine karo na 4 da kasar Indiya tayi gwajin makamanta tun 2002.Makamin mai linzami zai iya dauka ton daya na nukiliya wanda zai iya kaiwa kilomita 700.Kasar Pakistan makwabciya itama takan yi nata gwajin lokaci lokaci amma kuma dukkanisnu sai sun sanarda juna.