Indonesiya ta ce 'yan IS na kunyata Musulmi
August 21, 2014Talla
Mr. Yudhoyono ya ce irin yunkurin da 'yan IS din ke yi na kame yankuna da dama a Iraki da Siriya da ma salwantar rayukan mutane da ake samu sanadiyar wannan yunkuri nasu abu ne da ke da tada hankali matuka.
Shugaban na Indonesiya wadda ke zaman kasar da ta fi kowacce yawan musulmi a duniya ya ce halin da ake ciki yanzu kalubale ne ga shuganni da malaman addinin kuma loakci ya yi da za su zage damtse wajen yakar kaifin kishin addini.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu