Iraki ta ce Saudi da Qatar ne ke rura wutar rikicin kasar
March 9, 2014Talla
Al-Maliki ya ambata hakan ne a wata hira da aka yi da shi a jiya, daidai lokacin da Irakin ke cigaba da fuskantar hare-haren kunar bakin wake wanda kasar ba ta ga irinsa ba tun cikin skerara ta 2008.
Firaministan na Iraqi ya ce yanzu haka wadannan kasashe biyu na taimakawa 'yan tawayen kasar da kudade da kuma tallafi ta bangaren watsa labarai, lamarin da ya ce daidai ne da tallafawa aiyyukan ta'addanci a duniya.
Dama a cikin watan Janairun da ya gabata al-Maliki ya ambata cewar awkai wasu kasashen da ke dafawa 'yan bindigar kasarsa sai dai bai kai ga bayyana sunayen ba sai a jiya Asabar.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh