Iraki ta yaba salon yaki da ta'addanci na Trump
March 21, 2017Talla
Firaministan na Irki ya yi wannan kalami ne bayan ganawarsa da shugaban na Amirka a fadarsa ta White House ko kuma Maison Blanche, inda Shugaba Trump ya jaddada aniyarsa ta ganin bayan kungiyar IS yana mai cewa:
"Babban burinmu shi ne na kawo karshen kungiyar IS, kuma muna kan haka, za mu ga bayansu, domin Janar Mattis da tawagarsa suna aiki mai kyau. Abubuwa da dama sun sauya kan yadda a makwanni biyar zuwa shidan da suka gabata, don haka muna tare da ku, kuma mun gode da wannan ziyara ta Firaminista."
Bayan ganawarsa da Shugaba Trump, Firaministan na Iraki ya sanar cewa taimakon da Amirka ke bayarwa wajen kwato birnin Mosul na habaka cikin gaggawa a karkashin mulkin Shugaba Trump.