Yunkurin shawo kan masu zanga-zanga
October 10, 2022A karon farko tun bayan barkewar zanga-zanga a kasar Iran, babban Alkalin alkalan kasar ya yi kira na a hau kan teburin sulhu don ceto kasar daga durkushewa. Gholam-Hossein Mohseni-Ejei ya ce, 'yan kasa da bangaren gwamnati su sani cewar kofofi a bude suke don bayar da damar zama domin tattauna mafita daga halin rudanin da kasar ta fada ciki.
Zanga-zangar da ta ja hankalin duniya da kiraye-kiraye daga kasashen yamma na son ganin an sakar wa mata mara, ya yi sanadiyar rayukan mutum sama da arba'in baya ga wasu da dama da ake ci gaba da tsare da su a gidajen yari, mahukuntan na Tehran sun sha zargin wasu kasashe wadanda ba su da hannu a rura wutar rikicin kasar.
Sama da makonni uku kenan da zanga-zanga ta barke a kusan duk fadin Iran bayan mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini a lokacin da ta ke hannun jami'an Hisba, an dai tsare ta ne bisa laifin sabawa dokar sanya hijabi, lamarin da ya tayar da rikici, inda mata suka fantsama kan tituna suna nuna fushinsu kan mutuwar matashiyar da kuma adawa da dokar sanya hijabin .