Tehran na son a sakan mata mara
December 27, 2021Talla
Gwamnatin Tehran ta nunar da cewa, babban abin da take bukata a yarjejeniyar shi ne, ba ta damar sayar da albarkatun man fetur dinta da kuma yin amfani da kudin kasar da ke bankunan kasashen waje. Takunkuman da aka kakabawa Iran kan man fetur da kuma kudin da ta ajiye a bankunan kasashen ketare, sun takura Tehran matuka, abin da ya sanya tilas take son cimma yarjejeniya da kasashen masu fada a ji a duniya kan makamashin nukuliyarta.
Iran ta bukaci al'ummomin kasa da kasa, da su dage takunkumin da suka sanya mata a kan albarkatun man fetur dinta. Ministan harkokin kasashen ketare na Iran Hussein Amir-Abdollahian ne ya bayyana wannan bukata, yayin da aka koma kan teburin tattaunawa dangane da batun nukiliyarta a wannan Litinin.