Iran na zaben shugaban kasa
June 28, 2024Talla
Ana sa ran 'yan kasar miliyan 61 ne za su kada kuri'ar zaben sabon jagora bayan mutuwar Ebrahim Raisi a watan Mayun 2024, duk da cewa jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei shi ne mai cikakken fada a ji a Iran kana babban kwamandan rundunar sojin kasar.
Karin bayani: Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran
'Yan takara hudu ne za su fafata a zaben, sai dai wadanda ake ganin za su iya lashe zaben su ne Saeed Jalili, tsohon mai shiga tsakani a tattaunawar kasa da kasa a kan nukiliya da kuma Mohammad Bagher Ghalibaf, tsohon ministan kiwon lafiyan kasar.
Idan har babu dan takarar da ya samu rinjaye, za a sake komawa zagaye na biyu na zaben a ranar biyar ga watan Yuli.