SiyasaJamus
Iran ta nesanta kanta da zargin hallaka Donald Trump
November 9, 2024Talla
Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Iran a wata sanarwa da ta fidda a ranar Asabar ta ce ko kusa wannan zargin ba shi da tushe balle makama.
Sanarwar ta kara da cewar Iran ba ta da hannu a yunkurin kisan jami'an Amurka na da ko ma na yanzu.
Duk wannan na zuwa ne bayan da a ranar Juma'a masu shigar da kara a Amurka su ka sanar da daukar mataki a kan wannan zargin.
Danganataka a tsakanin Amurka da Iran ta jima da yin tsami, inda ko a baya-bayan nan Amurka ta sake laftawa Iran din wasu karin takunkumai a kan abin da ta kira na taimakawa mayakan Hizbullah kai wa Isra'ila hari.
Karin Bayani: Isra'ila ta ce ta kammala harin ramuwar gayya kan Iran