1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIran

Girka: Sakin jirgin dakon maai da Iran ta kwace

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 25, 2024

Iran ta saki jirgin ruwan dakon man fetur mallakin kasar Girka da ke dauke da tutar Tsibirin Marshall, wanda ta cafke a farkon wannan shekara ta 2024 da muke ciki a gabar ruwan Oman.

https://p.dw.com/p/4ikGh
Iran | Jirgin Ruwa | Dakon Man Fetur | Rikici
Da ma rikicin kwace tankokin dakon mai ba sabon abu ba ne a gabar ruwan na OmanHoto: Kostis Ntantamis/Sputnik Greece/IMAGO

Wata majiya ta zirga-zirgar jiragen ruwa ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters da sakin jirgin, sai dai kuma ta bayyana cewa har yanzu tankar dakon man kirar M/T St. Nikolas da jirgin ruwan dakon man fetur din ke dauke da ita na hannun mahukuntan na Tehran. Tankar dai na dauke da ganga miliyan daya ta danyen man fetur daga Iraki, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Turkiyya lokacin da Iran din da kwace shi a watan Janairun wannan shekara da nufin mayar da martani kan nata jirgin da Amurka ta kwace a bara kamar yadda kafar yada labaran Tehran din ta bayyana a wancan lokaci.