1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar IAEA ta ziyarci kasar Iran

February 22, 2021

Majalisar dokokin Iran ta shiga cikin dambarwa, bayan da hukumomin kasar suka sanar da gagarumar nasara a tattaunawar da suka yi da babban jami'in Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA.

https://p.dw.com/p/3pib8
Iran I International Atomic Energy Agency (IAEA)
Darakta janar na hukumar IAEA Rafael GrossiHoto: Hadi Zand/WANA/REUTERS

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta tura wakilin nata Iran ne, domin tabbatar da cewa Tehtran din ta bude tashoshin nukiliyarta ga masu bincike na duniya gabanin sake farfado da yarjejeniyar nukilyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya a 2015, wacce daga baya tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya fice daga cikinta. Ganawar da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA ta yi da Iran dai, ta samar da kwarin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.

Karin Bayani: Iran da hukumar IAEA sun cimma matsaya

A baya dai a Talatar wannan makon Iran din ta kuduri aniyar dakatar da duk wani rangadi da jami'an hukumar ta IAEA za su yi a cibiyoyinta da ake zargin tana sarrafa makaman nukiliya, domin tilastawa Amirka ta janye takunkuman da ta kakaba mata a kan batun.
Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran din Saeed Khatibzade ya ce tattaunawarsu da hukumar IAEA ta samar da kwarin gwiwa. A yanzu, Iran ta ce za ta ci gaba da bude wa masu bincike na Majalisar Dinkin Duniyar cibiyoyin nukiliyarta domin yin nazarin da ya kamata, amma ta ce  za ta hana su shiga cibiyoyinta wadanda ba na nukilya ba.

Iran I Teheran I Behrouz Kamalvandi und Rafael Mariano Grossi
Kakakin hukumar kula da nukiliyar Iran Behrouz Kamalvandi da Rafael Grossi na IAEAHoto: Atomic Energy Organization of Iran/AFP

Karin Bayani: Takunkumin Amirka kan Iran ya fara aiki

Dadin gushi ma mambobin majalisar kasar sun ce lallai Iran din ta tabbatar daga Talatar wannan makon za ta takaita cibiyoyin da jami'an na hukumar kula da makamashin nukiliyar ke duba wa. To amma  duk da haka a cewar Rafael Grossi da ke zaman darakata janar na hukumar ta IAEA da ya je birnin Tehran a Lahadin karshen mako  domin ganewa idanunsa, ganawar da aka yi ta samar da ci gaba. 
A shekara ta 2015 ne dai manyan kasashe shida masu fada a ji a duniya, suka cimma yarjejeniya da Iran din domin ta sassauto daga aikin bunkasa makamashin uranium wanda ke zama sinadarin samar da makaman nukiliya. Duk da cewa manyan kasashen shida masu fada a ji a duniyar sun sanya hannu kuma Iran din ta fara mutunta yarjejeniyar, amma a shekara ta 2018 tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya fice daga cikinta tare kuma da kara kakabawa Tehran din takunkumai kala-kala. 

Iran I International Atomic Energy Agency (IAEA)
Tattaunawar Rafael Grossi tare da tawagar Iran kan makamashin nukiliyaHoto: STR/AFP/Getty Images

Karin Bayani: Iran tana neman hanyar dakile takunkuman Amirka

A dangane da haka ne babban jami'in hulda da kasashen ketare na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce, suna kokarin ganin Amirka ta ci gaba da martaba yarjejeniyar nukiliyar. Ziyarar babban jami'in hukumar ta IAEA a Tehran din dai, ta sanya Iran din amincewa jami'anta su sanya na'urorin nadar bidiyo a cibiyoyinta na nukiliya har na watanni uku, amma ba za ta ba kowa bayannan ba har sai  Amirka ta janye mata takunkumi in ko ba haka ba ta goge bayanan.