IS ta rusa masallacin Al-Nuri a Iraki
June 22, 2017Talla
Kungiyar ta IS ta musunta zargi kana kuma ta dora alhakin rusa masallacin da hasumiyar sa a kan rundunar mayakan sama ta Amirka. janar Al Saadi na daya daga cikin mayan kwamandojin sojin na Iraki: '' Muna a kan hanyar zuwa Mosul inda masallacin Al Nuri yake, za mu samu nasara a kan yan IS.'' Rusa masallacin wanda ke cike da tarihi wanda aka gina tun a karni na tara na zuwa ne a kwanaki na hudu na hare-haren da sojojin Irakin ke kai wa a birnin na Mosul da nufin kwato shi daga cikin hannu 'yan tawayen.