1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Hamas na nazarin daftarin tsagaita bude wuta

February 2, 2024

Qatar da ke shiga tsakani ta ce Hamas ta amince da yarjejeniyar Paris na bukatar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni na makonni shida, duk da cewa ba a kai ga tsara jadawalin yadda yarjejeniyar za ta kasance ba.

https://p.dw.com/p/4bx5Q
Ministan harkokin Wajen Qatar, Majed Al-Ansari
Ministan harkokin Wajen Qatar, Majed Al-Ansari Hoto: Imad Creidi/REUTERS

Ministan harkokin wajen Qatar Majed al-Ansari, ya ce sun samu tabbacin amincewar daga Hamas kamar yadda hukumomin Isra'ila suka bada tabbacin amincewa da sabuwar yarjejeniyar.

Amurka da Masar da Qatar da ke shiga tsakani sun tattauna da hukumomin leken asirin Isra'ila a birnin Paris na kasar Faransa, tare da cimma matsayar tsagaita bude wuta na tsawon makonni shida.

Wata majiya daga Hamas ta sanar da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tsagaita bude wutan na sati shida zai ba da damar shigar da kayayyakin agaji da magunguna yankin na zirin Gaza.

Sai dai wata majiyar ta bayyana wa AFP cewa har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba kan yadda sabuwar yarjejeniyar za ta kasance.