Isra'ila ta kashe likitoci da dan jarida a Gaza
December 15, 2024Sojojin Isra'ila da ke zirin Gaza sun halaka akalla mutum 28 ciki har da dan jarida da ma'aikatan kiwon lafiya da kuma na jinkai.
Sai dai kuma sojojin na Isra'ila sun ce sun kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa a arewacin Gaza ne don halaka 'yan bindiga da kuma kama wasu.
Isra'ila ta aikata 'kisan kare dangi' a Gaza - Amnesty International
Jirgin yakin kasar ya yi ruwan wuta kan wata cibiyar agajin gaggawa a kasuwar Nuseirat da ke tsakiyar zirin inda ya kashe Ahmed Al-Louh dan jaridar kafar sadarwa ta Al Jazeera.
Akwai kuma wasu ma'aikatan kiwon lafiya da karin wasu 'yan jaridar da harin ya rutsa da su baya ga ma'aikatan agajin gaggawa da ke aiki a kasuwar da aka mayar sansanin jinya.
Isra'ila ta kai hari a iyakar Labanan da Syria
Al Jazeera ta fada cewa dan jaridan na tsakiyar aiki ne yayin da Isra'ila ta halaka shi. Sojojin na Isra'ila sun ce suna bin diddigin rahoton kisan dan jaridar.