Gaza: Isra'ila ta kubutar da 'yan kasarta a Rafah
February 12, 2024A sanarwar da ma'aikatan tsaron Isra'ila ta fitar ta ce mutanen biyu Fernando Simon Marman da Louis Har, na daga cikin mutanen da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba.
Sojojin Isra'ila na ci gaba da nausawa zuwa cikin birnin Rafah da ke kan iyakar Masar, birnin da daruruwan 'yan gudun hijra suka samu mafaka daga hare-haren Isra'ila.
Karin Bayani:Isra'ila ta umurci a kwashe fararen hula daga garin Rafah
Halin da ake ciki a yankin da kuma bukatar shigar da kayan agaHamas ta gargadi Isra'ila a kan shiga Rfahjin gaggawa ya sanya hukumomi da gwamnatocin kasashen duniya ciki har da babbar kawar Isra'ilan wato Amurka ci gaba da nuna damuwa kan fadada kai hare-haren Isra'ila yankin na Rafah.
Karin Bayani:Saudiyya ta bukaci a dakatar da Isra'ila daga shiga Rafah
Duk da matsin lamba daga kasashen duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, na ci gaba da jaddada kai farmaki yankin na Rafah, kamar yadda ya bada umarni ga sojojin Isra'ila da su kasance cikin shiri na shiga birnin.
Karin Bayani:Masar: Adawa da kwararar 'yan gudun hijira
Hare_haren Isra'ailan na daren litinin 12 ga watan Fabrairu, 2024, ya lalata gidaje akalla 14 da masallatai 3 a Rafah, acewar hukumomin yankin.