1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta mayar da 'yan gudun hijrar Afirka gida

Ramatu Garba Baba
April 13, 2018

Yuganda ta ce ta na nazari kan bukatar Isra'ila kafin ta amince da karbar 'yan gudun hijrar kasashen Eritrea da Sudan kusan500 da Isra'ilan ke son ta tsugunar a kasar.

https://p.dw.com/p/2w0uF
Israel Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/newscom/D. Hill/UPI Photo

Wakilan kasashen biyu sun shiga wata tattaunawa domin cimma matsaya kan batun yin na'am da bukatar amsar 'yan gudun hijrar, da yanzu haka ke zaune a Israila domin a basu mafaka a kasar ta Yuganda.

Wannan na zuwa ne bayan da a watan Janairun wannan shekara ta 2018 da muke ciki, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba wa 'yan gudun hijira mafi akasari wadanda suka fito daga kasashen Afirka zuwa Isra'ila ba bisa ka'ida ba zabin fita daga kasar cikin girma da arziki ko da karfin tuwo, matakin da ya fuskanci suka daga hukumomin kare hakin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin fararen hula da ke rajin kare hakkin dan Adam din a duniya.