1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila za ta shiga sulhun Masar bayan kashe jami'an jinkai

April 6, 2024

Wakilan Amurka da Isra'ila da Hamas za su isa birnin Alkahira na kasar Masar domin sake zaman sulhu tare da tsagaita bude wuta harma da musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/4eVUL
Wani zaman tattaunawa kan rikicin Gaza a Masar
Wani zaman tattaunawa kan rikicin Gaza a MasarHoto: Saudi Press Agency/APA/ZUMA/picture alliance

Jaridar Masar ta  Al-Qahera ta ce shugaban hukumar CIA na Amurka Bill Burns da Firaiministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani za su kasance a wajen zaman sulhun domin kawo karshen yakin na Gaza.

Karin bayani: Isra'ila ta kori sojojinta 2 da ladaftar da wasu 3 da suka hallaka jami'an agaji 7 a Gaza

Tattaunawar sulhun na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta amsa laifinta tare da daukar mataki na sallamar sojojinta biyu daga bakin aiki, bayan kashe jami'an agajin jinkan nan bakwai na 'World Central Kitchen', a daidai lokacin da suke tsaka da gudanar da aikin jinkai a Gaza.

Karin bayani: Isra'ila ta ce bisa kuskure ta kashe jami'an agaji a Gaza

Mayakan na Hamas tun bayan kaddamar da harin 7 ga watan Oktobar bara, sun yi garkuwa da 'yan Isra'ila kimanin 250 da har yanzu 130 na hannunsu, yayinda mutane 1,170 suka mutu. Kazalika Ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce Isra'ila ta hallaka kimanin mutane 33,137 a Gaza da galibinsu mata da kananan yara.