Iyalan da suka mayar da mulkin Afirka gado
A kasashen Afirka siyasa na zama tamkar gado: 'Ya'ya maza ka iya gadar mahaifinsu a shugabancin kasa, 'ya kuma shugabar hukumomin gwamnati, uwa kuwa minista. Ga wadansu misalai.
Dana mai tsaron lafiyata
Manjo janar Muhoozi Kainerugaba shi ne babban dan shugaban kasar Yuganda mafi dadewa a kan mulki Yoweri Museveni. Manjo janar ne a rundunar sojan kasar kana kwamanda mai kula da tsaron fadar shugaban kasa. Matar Museveni ita ce ministar ilimi da wasanni. Sirikinsa Sam Kutesa kuwa, ministan harkokin kasashen ketare.
'Yar shugaban kasa biloniya
Babbar 'yar shugaban kasar Angola Isabel dos Santos na daya daga cikin mutane 10 da suka fi arziki a Afirka. Tana mallakar babban kamfanin wayar sadarwa na kasar, kana shugabar reshen wani babban shagon saye da sayarwa a kasar. Ita ce shugabar kamfanin mai na kasar Sonangol. Dan uwanta José Filomeno shi ne shugaban asusun kasar FSDEA, da ke hada-hadar kudi sama da dalar Amirka miliyan biyar.
Babana na shirya ni…
Teodoro Nguema Obiang Mangue shi ne mataimakin shugaban kasa na biyu a Equatorial Guinea, kana dan shugaban kasa. Babansa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na shugabancin kasar tun daga shekara ta 1979. Dan matarsa Gabriel Mbega Obiang shi ne ministan albarkatun man fetur. Kamfanin mai na kasar GEPetrol na karkashin jagorancin sirikinsa Nsue Okomo.
'Yar uwa mai tasiri
Jaynet Désirée Kabila Kyungu 'ya ce ga tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango Laurent Kabila. Yanzu dan uwanta Joseph Kabila ke shugabancin kasar. Jaynet 'yar majalisa ce, baya ga haka tana da kamfanonin yada labarai. Bayanan badakalar "Panama Papers" ya nunar da cewa tana da hannun jari a wani babban kamfani, wanda Kwangon ka iya samun kudin shiga na haraji mai tarin yawa.
Daga sakatariya zuwa matar shugaba
Grace Mugabe ita ce matar shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe da ya dade a kan karagar mulki ta biyu. Dangantakarsu ta fara ne tun lokacin tana sakatariyarsa kana shugabar mata ta jam'iyya mai mulki. A yanzu ana tunanin Grace da ke da shekaru 51 ka iya gadar mijinta a matsayin shugabar kasa, wanda ke da shekaru 92 a yanzu haka a duniya.
Tsohuwar matar shugaban kasa mai buri
Nkosazana Dlamini-Zuma ce mace ta farko da aka zaba a matsayin shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Afirka. Ita ce mace ta farko da ta zama ministar kasashen ketare karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki kafin ta zama ministar cikin gida a gwamnatin tsohon mijinta Jacob Zuma, wanda suka rabu kafin ta zama minista. A yanzu tana fatan zama shugabar kasa.
Fadar gwamnati a matsayin kamfanin iyali
Manya da muhimman kamfanoni da mukamai na hannun iyalan shugaban kasar Kwango Brazzaville Denis Sassou-Nguesso. 'Yarsa Claudia (da ke cikin wannan hoto) ita ce shugabar sashen yada labarai na mahaifinta. Dan uwansa Maurice na da manyan kamfanoni, kana yana shirya dansa Denis Christel domin ya gaje shi a mulki.
An amince da Shugaba Bongo na biyu
Tsawon shekaru 41 Omar Bongo Ondimba ya kwashe yana shugabancin kasar Gabon, tun daga shekarar 1967 zuwa 2009. A wani zabe mai cike da rudani da aka gudanar a kasar a karon farko, inda aka amince da wanda ya samu rinjaye a zagayen farko, dansa Ali Bongo ya dare kan karagar mulki. A shekara ta 2016 an sake zabarsa a matsayin shugaban kasa. Iyalan Bongo sun kwashe rabin karni suna mulki a Gabon.
Barewa bata gudu danta ya yi rarrafe
Daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban kasar Togo Gnassingbé Eyadéma da ya kwashe tsawon shekaru yana mulki, dansa Faure Gnassingbé ne kadai ya shiga harkokin siyasa. A yanzu shi ne shugaban kasar. Haka ma a Kenya da Botswana, wadanda ke shugabanci a wadannan kasashen, iyayensu ma sun yi shugabancin kasashen nasu.