Nijar: Majigi domin rijistar masu zabe
October 16, 2019Hukumar ta CENI a Nijar dai ta ce ta yanke shawarar amfani da allon majigin ne a manyan filaye, domin bai wa al'umma damar fayyace yadda ake rijistar katin zaben, duba da yadda a wannan karon aka shigo da shirin na'urori wajen yi wa masu zaben rijista. Wannan dai shi ne karo na farko da hukumar zaben ta kasa CENI a Jamhuriyar ta Nijar ta shigo da shirin amfani da allon majigi wajan kwatanta wa al'umma matakai dabam-dabam na yin rijistar da na'urorin da aka shigo da su, ganin yadda lokaci ke kara karatowa inji Maman Sani Moussa shugaban hukumar reshen jihar Tahou.
To sai dai duk da wannan yunkurin da ake gani a matsayin wani muhimmin ci-gaba, wasu kuwa na ganin bai gamsar da su ba ganin yadda ake fuskantar kura-kurai a yanzu haka. A nasa bangaren gwamnan jihar ta Tahoua Alhaji Abdouramane Moussa ya yi kira ga al'umma da su yi amfani da wannan damar wajen shaidawa 'yan kasar muhimmancin katin zaben da ya kasance 'yancinsu. Tuni dai aka kaddamar da shirin rijistar a duk fadin kasar tun a farkon wannan mako da muke ciki, koda yake ana cin karo da kalubalen rashin zuwan mutane da ma tangardar wasu daga cikin na'urorin.