1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'ai na share wa Trump da Kim hanya

Yusuf Bala Nayaya
May 29, 2018

Babban mai taimaka wa Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya isa Singapoor a daren Litinin kamar yadda kafar yada labaran kasar Japan NHK ta bada labari a wannan rana ta Talata.

https://p.dw.com/p/2yUWW
USA Nordkorea - Donald Trump und Kim Jong Un - TV
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Jin-man

Wannan dai wani mataki ne da ake kallo na kara share hanyar yiwuwar tattaunawa tsakanin ShugabaTrump da Shugaba Kim. Kim Chang Son da ake kallo a matsayin shugaban ma'aikata na Shugaba Kim ya je Singapoor bayan ratsa Beijing a daren na Litinin kamar yadda rahoto ya nunar.

Wani rahoton kuma ya nunar da cewa tawagar jami'an diflomasiya daga Amirka da ake sa rai za su shiga wannan tattaunawa sun bar wani otel a birnin Seoul na Koriya ta Kudu a wannan Talata, abin da ke zuwa yayin da ake rade-radin cewa za su fara tattaunawa. An kuma gano wani babban janar din soja na Koriya ta Arewa Kim Yong Chol ya sauka a Beijing na China a wannan Talata inda daga nan zai nufi birnin Washington na Amirka.

Har ila yau wasu rahotannin sun nunar da cewa Shugaba Donald Trump ya gana da Firaminista Shinzo Abe na Japan kuma a tattaunawar da suka yi ta wayar tarho Trump da Abe, sun amince kan muhimmancin ganin an kawar da shirin makamin nukiliyar Koriya ta Arewa da duk wasu makamai masu hadari da kasar ke da su. Shugabannin biyu kuma sun tsara za su gana gabannin tattaunawar ta Trump da Kim.