1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China da Philippines sun yi arangama a Tekun Kudancin China

December 4, 2024

China ta yi zargin cewa jiragen ruwan Philippines sun yi yunkurin shiga yankinta yayin da masu gadin Tekun Philippines ke zargin takwarorinsu na China da kai wa jirginsu hari.

https://p.dw.com/p/4niUU
Takaddama kan Tekun kudancin China
Takaddama kan Tekun kudancin ChinaHoto: PHILIPPINE COAST GUARD/AP Photo/picture alliance

Kasashen China da Philippines na zargin juna da takalar fada bayan da jami'an tsaron gabar Teku na kasashen biyu suka yi arangama a ranar Laraba a Tekun Kudancin China wanda suke takaddama a kansa. 

Karin bayani: China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa

A cikin wata sanarwa jami'an tsaron gabar Teku na China sun yi watsi da zargin da Philippines ta yi musu na cewa sun harbi wani jirgin ruwanta lamarin da ya haddasa kifewarsa. Jami'an na China sun ce jirgin ruwan na Philippines ya kife ne sakamakon karo da ya yi da gangan da wani jirgin ruwa mallakin Beijing a wata kusurwa ta Tekun.

Kazalika sanarwar da kuma zargi Philippines da kitsa makirci don kara samun goyon bayan kasashen duniya kan takaddamar da ta barke a tsakanin su a baya-bayan kan 'yancin mallakar wani bangare na Tekun Kudancin China.