1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta samu sabonn shugaban kasa

May 25, 2020

Evariste Ndayishimiye dan takarar jam'iyya mai mulki a zaben kasar Burundi ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Laraba da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3ck6j
Burundi Evariste Ndayishimiye zum Sieger der Präsidentenwahl erklärt
Hoto: Reurters/E. Ngendakumana

Hukumar zaben kasar ta ce Evariste Ndayishimiye ya samu kaso 68.72 na kuru'un da aka kada, lamarin da ya ba shi damar lashe zaben shugaban kasar ta Burundi.

Hukumar zaben ta ce madugun adawa Agathon Rwasa da ya yi takara a jami'iyyar National Freedom Council ya samu kaso 24.19 na kuru'un da aka kada. Sai dai ba da jimawa ba madugun adawar da jam'iyyarsa sun yi watsi da sakamakon zaben, suna zargin an yi danniya da munakisa a zaben shugaban kasar. Jam'iyyar ta National Freedom Council ta yi zargin hukumomi sun kame wakilanta a rumfunan zabe don bayar da damar rubuta irin sakamakon zaben da ake so.

Zaben na Burundi dai ya gudana ba tare da masu sanya ido daga kasashen ketare ba a saboda annobar coronavirus.