1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Saliyo ta koma hannun jam'iyya mai mulki

Abdul-raheem Hassan
June 14, 2019

Jam'iyyar da ke mulki a kasar Saliyo ta yi nasarar kwace kujeru mafi yawa a majalisar dokokin kasar daga babbar jam'iyyar adawa bayan hukuncin wata kotu da ta soke sakamakon wasu mazabu.

https://p.dw.com/p/3KRoG
Sierra Leone Julius Mada Bio Präsidentschaftskandidat
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A wani mataki na mai abu ya rantse maras abu ya ranste. Jam'iyyun siyasa a kasar Saliyo na zargin juna da bita da kullin siyasa, inda babbar jam'iyyar adawa a kasar APC ta rasa kujeru masu yawa a majalisar dokoki bayan wani hukuncin kotun sauraron korafin zabe. Sai dai kakakin ma'aikatar shari'ar kasar Moses Kamara ya ce an yanke hukuncin ne bisa shaidun da aka gabatar.

A yanzu haka dai an rantsar da 'yan majalisu 9 na jam'iyyar SLPP mai mulki, yayin da za a sake gudanar da zabe guda daya. Ismael Mammie lauya ne a birnin Freetown da ke ganin hukuncin kotun na da tsarkakiya. Tuni bangaren babbar jam'iyyar adawa ta APC a Saliyo, ta ce hukuncin kotun ba ya kan tsari da gaskiya.

Hukuncin kotun da ya soke nasarar zaben wasu 'yan majalisun babbar jam'iyyar adawa, tare da ba da damar rantsar da yan majalisun jam'iyya mai mulki ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin 'yan siyasa da magoya baya, wannan na faruwa mako guda bayan da kasar ta gudanar da tuntubar zaman lafiya a duk sassan kasar ta Saliyo.