1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MPN ta jingine adawa da gwamnatin Bazoum

Salissou Boukari RGB
April 15, 2022

Jam'iyyar adawa ta MPN da ta yi kaurin suna wajen sukar lamirin gwamnatin Nijar ta yanke shawarar mara wa Shugaba Mohamed Bazoum baya don ci gaban kasar.

https://p.dw.com/p/4A0KI
Niger Wahlkampf - Mohamed Bazoum
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Jam’iyyar adawa ta MPN Kishin kasa ta Ibrahim Yacouba, da ta yi kaurin suna wajen caccakar gwamnati, ta yanke shawarar komawa bangaren gwamnati, inda ta ce, ta yi ne domin ta taimaka wa shugaban kasa Mohamed Bazoum bisa kyakyawar niyar da yake da ita ta kawo sauye-sauye a Nijar. Sai dai wannan mataki ya farfado da shakkun da jama’a suke da shi kan kalaman 'yan siyasar ta Nijar da akidunsu. 

Tun da dadewa ne ake rade-radin cewa jam’iyyar MPN Kishin kasa dai ungulu ce da kan zabo a bangaren jam’iyyun adawa kasar ta Nijar har ya zuwa yammacin ranar Alhamis da ta gabata, inda wani taron uwar jam’iyyar da ya hada dukannin masu fada da juna a jam’iyyar daga sauran jihohi suka amince da mara wa gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum baya.

Präsidentschaftskandidat Ibrahim Yacouba Niger Wahl 2016
Ibrahim Yacouba na jam'iyyar MPNHoto: DW/M.Kanta

Sai dai daga bangaren 'yan kungiyoyin fararan hula yayin da wasu ke ganin cewa matakin na MPN Kishin Kasa bai ba su mamaki ba, wasu na ganin cewa a nan gaba da wuya al’umma ta yarda da duk wani kalami na 'yan siyasa a kasar ta Nijar wanda yau idan sun ce baki ne gobe kuma su ce fari ne.  Yanzu dai abun jira a gani shi ne ko jam’iyyar ta MPN Kishin kasa ta yi wannan bulaguro ne daga adawa zuwa bangaren masu mulki don ita ma ta sha mimido kamar yadda ake fada, ko kuma ta yi ne kawai bisa nuna kishin kasa kamar yadda sunan jam’iyyar ya nunar.