1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Jam'iyyar PDP na fama da rikici

Uwais Abubakar Idris LM
September 20, 2024

Rikicin cikin gida na babbar jamiyyar adawa ta PDP a Najeriya ya kara daukan sabon salo, inda gwamnonin jam'iyyar suka rabu biyu a kan batun shugabancin Umar Iliya Damagun da fiye da shekara guda ke nan.

https://p.dw.com/p/4kv1d
Najeriya | Rikici | PDP
Lemar jam'iyyar PDP na dab da yagewa a NajeriyaHoto: DW/K. Gänsler

Kura dai da sake turnukewa ne a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ta PDP mai adawa a Najeriyar, a kan shugabanta na riko Umar Iliya Damagun da ya dare mukamin saboda guguwar da ta yi awon gaba da tsohon shugabanta Iyorchia Ayu. Sai dai rikon ya yi tsawo, bayan da kwamitin zartaswwar jamiyyar ya ba shi ikon ci gaba da zama kan wannan matsayi. To sai dai a yanzu wuta ta sake tasowa, inda gwamnonin jam'iyyara da a ba ya ake kalon su a matsayin tsintsiya madauranlki daya suke fuskantara rarrabuwar kawuna tare da hango su a rana a kan shugabancin jamiyyar. Wasu gwamnonin dai na da ra'ayin tilas sai shugaban na riko ya sauka, domin mayar da shugabancin zuwa sashin Arewa maso Tsakiyara Najeriya. Rikici ne dai da ake danganta shi da ministan Abuja Nyesom Wike da shugaban jam'iyyar ke da kaykkyawar alaka da shi, abin da ake bayyanawa da irin gagarumin tasirin da Wike ke da shi a PDP.

Najeriya I PDP | Nyesom Wike
Ministan Abuja a Najeriya kana jigo a jam'iyyar adawa ta PDP Nyesom WikeHoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Ana dai yi wa Wike kallon wanda ya raba kafa tsakanin jam'iyyarsa ta PDP da APC mai mulki da ta bashi mukamin minista, bayan bijirewar da ya yi a lokacin zaben shugaban Najeriyar. Tuni dai PDP ta fara nuna ta maza, inda ta dakatara da Sanata Dino Melaye daga jam'iyyar a mataki na tauna tsakuwa ko aya za ta ji tsoro. Farfesa Abubakar Umar Kyari masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja, ya ce wannan rikici na PDP na da illa, a matsayinta na babbar jam'iyyar adawa a Najeriyar. Bangaren shugaban jam'iyyar da masu goyon bayansa sun ja daga a kan wannan lamari, duk da kurar da ta taso a  yanzu da a fili ke tasiri ga yadda ake kallon PDP a matsayin babbar jagora a bangaren adawa. Masana kimiyyar siyasa na masu bayyana cewa, rashin kwanciyara hankali a cikin jam'iyyar da ke adawa da gwamnati babban cikas ne ga tsarin dimukurdiyya da ya ginu kan adawa mai karfi wacce ita ce gishin tsarin.